16 Mayu 2020 - 06:26
Iran: Mutane 91,836 Sun Warke Daga Cutar Corona A Kasar Iran

A ci gaba da nasarorin da ake samu a ƙasar Iran a faɗar da ake yi da cutar nan ta COVID-19, Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta ƙasar Iran ta sanar da cewa mutane 91,836 daga cikin mutane 116,635 da suka kamu da cutar sun sami sauƙi a ƙasar.

(ABNA24.com) A ci gaba da nasarorin da ake samu a ƙasar Iran a faɗar da ake yi da cutar nan ta COVID-19, Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta ƙasar Iran ta sanar da cewa mutane 91,836 daga cikin mutane 116,635 da suka kamu da cutar sun sami sauƙi a ƙasar.

Yayin da yake sanar da hakan a yau ɗin nan Juma’a, Kakakin Ma’aikatar kiwon lafiya ta ƙasar ta Iran Kianoush Jahanpour ya ce bisa ga kididdigar da aka tattaro daga jiya zuwa yau Juma’a 15 ga watan Mayu, adadin mutanen da suka kamu da cutar a ƙasar sun kai mutane 2,102 wanda hakan ya sanya adadin waɗanda suka kamu da cutar tun bayan ɓullarta zuwa yau sun kai mutane 116,635.

Kakakin Ma’aikatar lafiya ya ƙara da cewa: Abin farin cikin shi ne cewa cikin waɗannan adadin da suka kamu da cutar, 91,836 sun sami sauƙi kuma tuni aka sallame su, sai dai ya ce ya zuwa jiya zuwa yau ɗin mutane 48 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar wanda hakan ya sanya adadin waɗanda suka rasu tun farkon ɓullar cutar ya kai mutane 6,902.

Iran dai tana ci gaba da samun nasarorin gaske a faɗar da take yi da cutar ta Coronavirus sakamakon namijin ƙoƙarin da mahukuta da malaman jiyya suke yi a ƙasar lamarin da ya sanya yanzu adadin waɗanda suke ɗauke da cutar a ƙasar ba su ɗara mutane 2,727 kamar yadda kakakin Ma’aikatar lafiyan ƙasar ya sanar ba.


/129